✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Koriya ta Arewa: Yadda ake bikin cika shekara 10 da mulkin Kim Jong Un

An sauke tutoci kasa-kasa a birnin Pyongyang domin alhinin rasuwar marigayi Kim Jong Il.

Koriya ta Arewa na bikin cikar shugaban kasar, Kim Jong Un, shearka 10 a kan mulkin, gami da tunawa da rasuwar mahaifinsa tsohon Shugaba Kim Jong Il.

An saukar da tutoci kasa-kasa a birnin Pyongyan a ranar Juma’a a yayin da Shugaba Kim Jong Un da al’ummar kasar ke durkusawa a gaban hoton mahaifin nasa da kakansa Kim Il Sung, wasu kuma suna ajiye musu furanni a wurareen da aka ware a fadin kasar.

Marigayi Shugaba Kim Jong Il ya mulki Koriya ta Arewa na tsawon shekara 17 kafin rasuwarsa a watan Diasman 2011, wanda bayan nan dansa Kim Jong Un ya maye gurbinsa.

Shugaba Kim Jon Un da dubban al’ummar kasar ne ke halartar bikin da ke gudana a ranar Juma’a a fadar ‘Kumsusan Palace of the Sun’, wadda aka tsara domin tunawa da Kim Jong Il da mahaifinsa Kim Il Sung — wanda shi ne ya kirkiro da kasar Koriya ta Arewa.

— Koriya ta Arewa karkashin mulkin zuri’ar Kim

Daga shekarar 1948 zuwa yanzu, zuri’a uku ke nan daga dangin Kim suka mulki kasar Koriya ta Arewa.

Al’ummar kasar na girmamam Kim Il Sung da da dansa matuka, inda tun yara suna kanana ake koya musu haka, manya kuma suke sanya baje a kayansu, dauke da hotunansu ko daya daga cikinsu.

Munate sun rankwafe domin girmama Shugaba Kim Il Sung da Kim Jong Il, a bikin cika shekara 100 da rasuwar Kim Jong Il, mahaifin Kim Jong Un, a birnin Pyongyang, ranar Juma’a 17 ga Disamba 2021. (Hhoto: KIM Won Jin/AFP).

A karkashin mulkin zuri’ar Kim ne kasar ta fara kera makamai masu cin dogon zango da makami mai linzami da Nukiliya.

Sai dai a bangaren tattalin arziki, ana fama da rashin wadataccen abinci.

Kim Jong Un ya ce yana sane da halin da jama’ar kasar suka tsinci kansu, amma ya shawarce su da su kara jajircewa.

A bara kasar ta rufe iyakokinta domin hana shigowar cutar COVID-19, matakin da ya kara wa matsalar tsanani.

Kafin nan, kasar na fama da tasirin takunkumin da kasashen duniya suka sanya mata saboda shirinta na kera makamai.