✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Koriya ta ba ma’aikatan Najeriya tallafin amawali

Kasar Koriya, ta hannun Hukumar Agajin ta mai suna (KOICA) ta bai wa ma’aikatan Najeriya kyautar amawali domin hana yaduwar cutar COVID-19. Shugaban makarantar ma’aikatan…

Kasar Koriya, ta hannun Hukumar Agajin ta mai suna (KOICA) ta bai wa ma’aikatan Najeriya kyautar amawali domin hana yaduwar cutar COVID-19.

Shugaban makarantar ma’aikatan Najeriya, Abdul-Ganiyu Obatoyinbo ya karbi kayan da aka kawo, kamar yadda yake kumshe a takardar da hukumar ta fitar ranar Laraba.

Da yake jawabi a wajen taron, shugaban KOICA na Najeria Mista Woochan Chang, ya ce sun yi hakan ne domin taimaka wa yaki da cutar da kuma taimaka wa abokan huldarsu a lokacin tsananin da ake ciki.

Mista Woochan ya ce, agajin ya zo a lokacin da ya dace domin taimakawa a ranar amawali ta duniya da kuma gangamin #MaskOnNaija na ba wa mutane kwarin gwiwar yin da amawalin don kariya daga COVID-19.

Shugaban makarantar ya gode wa hukumar da daukin, tare da cewa takunkumin zai taimaka sosai wajen hana yaduwar annobar.