✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Kotu ta aike da Shugaban EFCC gidan yari

Kotun ta ba da umarnin a tsare shi a kurkukun Kuje na tsawon kwana 14

Babbar Kotun jihar Kogi ta ba da umarnin aikewa da Shugaban Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta EFCC, Abdulrasheed Bawa, gidan gyaran hali saboda kin bin umarnin kotu.

Alkalin kotun, Mai Shari’a R.O. Ayoola ne ya bayar da umarnin a yayin zaman kotun na ranar Litinin.

Kotun ta kuma umarci Babban Sufeton ’Yan Sandan Najeriya, da ya kama tare da tasare Abdulrasheed din a gidan gyaran hali na Kuje har na tsawon kwana 14, har sai ya kare kansa daga zargin rashin da’ar.

Da yake yanke hukuncin, Alkalin ya amince da bukatar aikewa da Bawan gidan yari kan hukuncin da aka yanke na ranar 30 ga watan Nuwamban bara.

A lokacin dai, wani mai suna Ali Bello ne ya maka Abdulrasheed din a gaban kotun kan kama shi tare da tsarewa ba bisa ka’ida ba, bayan lauyansa, S.A. Abass ya shigar da karar.

Kotun dai ta amsa bukatar Alin, amma sai EFCC ta gurfanar da shi a gaban kuliya kan zargin almundahana, kwana uku bayan yanke wancan hukuncin.

Tun a baya dai, kotun ta ayyana kamawa da kuma tsare Ali Bello a matsayin wanda ba ya kan ka’ida saboda an yi shi ne ba tare da umarnin kotu ba, sannan ya saba wa hukuncinta.

Bugu da kari, kotun ta kuma umarci masu kare kansu da su wallafa ban-hakuri a wata jarida ta kasa sannan su ba wanda ya yi kara diyyar Naira miliyan 10.