Kotu ta aike da yaran da suka kashe tsoho mai shekara 70 kurkuku | Aminiya

Kotu ta aike da yaran da suka kashe tsoho mai shekara 70 kurkuku

Kotu
Kotu
    Rahima Shehu Dokaji

Wata kotun majistare da ke Makurdi, babban birnin Jihar Binuwai, ta ba da umarnin tusa keyar wasu yara biyu gidan kaso bisa zargin kashe wani tsoho mai shekaru 70 ta hanyar duka.

’Yan sanda dai na zargin yaran masu suna Kwaghfan da Terkuma Kyooso, wadanda suka fito daga Gabashin Karamar Hukumar Binuwai da hadin kai a aikata ta’addanci da kuma kisan kai.

Alkalin kotun, Mai Shari’a Vincent Kor ne ya yanke hukuncin sannan ya dage ci gaba da sauraron karar zuwa ranar 18 ga watan Yulin 2022.

Tun farko dai lauyan masu kara, Insfekta Godwin Ato ya shaida wa kotun cewa ranar 30 ga watan Afrilu an kawowa kwamishinan ’yan sandan Jihar rubutaccen korafi kan laifukan hadin kai a aikata manyan laifuka, da keta, da kuma aikata laifin kisan kai da gangan, da kuma fashi da makami.

Wani dan mamacin mai suna Charles ne dai ya shigar da korafin a rubuce kan kisan mahaifin nasa mai suna Atule ranar 29 ga watan Afrilun 2022.

Zargin da ake wa yaran dai ya saba da sashe na 97 da na 222 na kundin dokokin penal code na shekarar 2004 na jihar Binuwai.