✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta amince da dokar hana dalibai sanya hijabi a Indiya

Kotun ta yanke hukuncin ne bayan shigar da kara a gabanta ana kalubalantar dokar.

Wata kotu a Kudancin Indiya ta amince da dokar hana mata musulmi sanya hijabi a makarantu a duk fadin kasar.

Kotun ta yanke hukuncin ne bayan shigar da kara a gabanta ana kalubalantar dokar.

Bayan an jima ana cece-kuce kan umarnin gwamnati na hana sanya hijabi a aji, a ranar Talata wata kotu a kasar Indiya ta amince da dokar hana mata musulmi sanya hijabi a makarantu.

Kotun da ke Jihar Karnataka a Kudancin kasar inda rikicin ya samo asali, ta yanke hukuncin bayan shigar da kara a gabanta ana kalubalantar dokar.

A watan Fabrairun da ya gabata, zanga-zangar dalibai mata musulmin ta barke kan batun hana matan sanya hijabi, batun da ya ja hankalin duniya tare da janyo rufe manyan makarantun sakandare da kuma kwalejoji a sakamakon rikicin da ya barke kan haramcin hijabin.

A watan ne kuma a rika kai ruwa rana kan batun hijabin musamman a Jihar Karnataka wanda ya jefa fargaba a zukatan Musulmai da dama da ke zargin gwamnatin Fira-Minista Narendra Modi da ci gaba da musguna musu.

A wancan lokaci ne dai Ministan Ilimin kasar, Basavaraj Bommai, ya yi kira da a kwantar da hankula, bayan ya sanar da cewa za a rufe dukkan manyan makarantun Jihar na tsawon kwana uku.

Dalibai dai a manyan makarantun gwamnati ba su da damar sanya hijabi a wata sabuwar doka da aka kafa a watan Janairun da ya gabata a jihar, kafin daga bisani sauran jihohi su ma su yi koyi wajen fara amfani da ita.