✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta ba da belin ‘Dansarauniya’ a kan N1m

Kotun ta bayar da belin nasa ne saboda rashin lafiya.

Wata kotun majistare da ke zamanta a unguwar Nomansland a birnin Kano ta bayar da belin tsohon Kwamishinan Ayyuka na Jihar, Injiniya Mu’az Magaji, wanda aka fi sani da Dansarauniya a kan Naira miliyan daya.

Alkalin kotun, Mai Shari’a Aminu Gabari, ne ya bayar da belin ranar Juma’a, bisa dalilan rashin lafiya.

To sai dai kotun ta umarci wanda ake zargin da ya mika mata fasfo dinsa na tafiya sannan ya kawo mutum biyu da za su tsaya masa.

Daga cikin mutanen da kotun ta shardanta su tsaya wa tsohon Kwamishinan har da Dagacin garinsa na Sarauniya da kuma Kwamandan Hisbah na Karamar Hukumar Dawakin Tofa, ko babban limamin garin.

Kotun ta kuma dage ci gaba da sauraron karar har zuwa ranar biyu ga watan Maris din 2022 mai zuwa.

A farkon makon nan dai, sai da kotun ta bayar da umarnin tsare Dansarauniya a gidan gyaran hali.

Ana dai tuhumarsa ne da laifuka hudu da suka jibanci bata suna, kokarin yin yarfe da gangan, yin karya da kuma neman yada kin jinin Gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje a idon jama’a.

An dai kama shi ne ranar Juma’a a Abuja, jim kadan daga firowarsa daga wani shirin tattaunawa na gidan talabijin na Trust TV.

Daga bisani an tiso keyarsa zuwa Kano a ranar sannan aka gurfanar da shi a gaban kotun.