✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Kotu ta ba da belin masu barazanar yada hotunan tsiraci

Wata kotun majistare da ke Legas ta ba da umarnin tsare wasu matasa biyu da suka yi barazanar yada hotunan wata mata tsirara a shafukan…

Wata kotun majistare da ke Legas ta ba da umarnin tsare wasu matasa biyu da suka yi barazanar yada hotunan wata mata tsirara a shafukan sada zumunta.

Matasan masu shekaru 23 ana tuhumar su ne da laifin daukar makwabciyarsu hoto tsirara ba tare da saninta ba, sannan suka bukaci ta ba su N200,000 ko su yada ta a kafafen sada zumunta.

Sai dai wadanda ake tuhumar sun musanta zargin, kuma Alkalin kotun, Misis B. O. Osunsanmi, ta ba su beli kan N3000,000, da masu tsaya musu da suka mallaki makamancin kudin.

Daga nan ta dage sauraron shai’ar zuwa ranar 6 ga watan Fabrairun shekarar 2023.