✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta ba da umarnin rage albashin ’yan Majalisar Tarayya

Wannan umarni ya wajaba bisa la’akari da matsin tattalin arziki da kasar ke fama da shi.

Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Legas, ta umarci Hukumar Karba da Tsara Albashi, RMAFC, da ta yi wa albashi da alawus-alawus na yan Majalisar Tarayya gyaran fuska.

A halin yanzu akwai ’yan Majalisar Tarayya guda 469 da suka hada da mambobi 109 a Majalisar Dattawa yayin da ita kuwa Majalisar Wakilai take da mambobi 360.

Kotun wacce Mai Shari’ah Chuka Austine Obiozor ya jagoranci zaman yanke hukuncin, ta ce wannan umarni ya wajaba ne bisa la’akari da matsin tattalin arzikin da kasar ke fama da shi.

Haka kuma, hukuncin da kotun ta yanke ya jaddada cewa Hukumar Kula da Ayyukan Majalisar Tarayyar ba ta da ikon kayyade albashi da alawus-alawus na ’yan majalisar.

Hukuncin ya biyo bayan karar hadin gwiwar da wani mai suna Mista Monday Ubani, da Mista John Nwokwu, da wadansu mutum fiye da 1,500 suka shigar tare da Kungiyoyin Rajin Tabbatar da Daidaito irin su, SERAP, da BudgIT da Enough is Enough Nigeria (EiE).

Kotun ta kuma yanke hukuncin cewa Hukumar RMAFC ita ce kadai ke da ikon kayyade albashi da sauran alawus-alawus na ’yan majalisar da sauran masu rike da mukaman siyasa.