✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Kotu ta ba da umarnin rataye mijin da ya kashe ‘kwarton’ matarsa

An same shi da laifin kashe wanda yake zargi da kwartancin

Wata babbar kotu da ke Aiyetoro a Jihar Ogun ta yanke wa wani mutum mai suna Adelake Bara hukuncin kisa ta hanyar rataya saboda samun sa da laifin kashe wani mutum da ya zarga da yin kwartanci ga daya daga cikin matansa guda uku.

Kotun dai ta yanke masa hukuncin ne ranar Litinin bayan samun sa da laifin kashe mutumin mai suna Olaleye Oke.

Da take yanke hukuncin, alkalin kotun, Mai Shari’a Patricia Oduniyi, ta ce ta yanke hukuncin ne bayan gamsuwa da hujjojin da aka gabatar mata cewa wanda ake zargin ya aikata kisan.

Alkalin ta ce laifin ya saba da tanade-tanaden Kundin Manyan Laifuka na Jihar ta Ogun.

Yayin shari’ar dai, lauya mai shigar da kara, Misis T.O. Adeyemi, ta ce mutumin ya aikata laifin ne da misalin karfe 6:00 na yammacin daya ga watan Mayun 2018 a unguwar Afodan da ke Ijoun a yankin Aiyetoro na Jihar.

Lauyar ta ce wanda aka yanke wa hukuncin ya aikata kisan ne lokacin da ya hadu da Olaleye a gonarsa.

“Adelake, wanda ke da mata uku ya fito da bindiga sannan ya harbi Olaleye a ka, lokacin da yake kokarin kare kansa cewa bai aikata abin da yake zarginsa da aikatawa ba,” inji lauyar.

Ta ce harbin da aka yi wa Olaleye a kan shi ne ya yi sanadiyyar mutuwar shi nan take. (NAN)