✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta ba da umarnin tsare Babban Hafsan Sojin Kasa

Za su ci gaba da kasancewa a tsare a gidan yari har sai sun wanke kansu daga laifin saba umarnin kotu

Babbar Kotun Jihar Neja ta ba da umarnin tsare Babban Hafsan Sojin Kasa na Najeriya, Janar Faru Yahaya, a gidan yari.

Mai Shari’a Halima Abdulmalik ta ba da umarnin tsare Babban Hafsa Sojin Kasan ne tare da Kwamandan Rundunar Soji ta TRADOC da ke Mina a Jihar Neja, kan kin bin umarnin kotu.

“Kotu ta ba da umarnin tsare Babban Hafsan Sojin Kasa na Najeriya, Janar Faruk Yahaya da Kwamandan Rundunar TRADOC da ke Minna a gidan yari, saboda saba umarnin wannan kotun na ranar 12 ga watan Oktoba, 2022.

“Za su ci gaba da kasancewa a tsare a gidan yari har sai sun wanke kansu daga laifin saba umarnin kotu,” in ji sanarwar kotun.

Ta ba da umarnin ne a shari’ar da wani mai suna Adamu Makama da wasu mutum 42 ke kalubalantar Gwamnan Jihar Neja da wasu mutum bakwai.

Lauyan masu kara, Mohammed Liman, ya bukaci kotun ta tisa keyar Babban Hafson Sojin Kasa na Najeriya, Janar Faruk Yahaya zuwa gidan yari ne saboda saba umarnin da ta bayar a watan Oktoba.

Kotun ta ba da umarnin ne kwanaki kadan bayan umarnin tsare shugaban hukumar EFCC a gidan yari kan irin wannan laifi.