✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Kotu ta ba da umarnin zabtare N40bn daga asusun Jihar Ebonyi

Kotu ta ce Gwamnatin Ebonyi ba ta yi wa kamfani da ta bai wa kwantaragi adalci ba.

Wata Kotun Tarayya mai zamanta a Fatakwal babban birnin jihar Ribas, ta bai wa Babban Bankin Najeriya (CBN) umarnin zabtare sama da biliyan 40 daga asusun Gwamnatin Jihar Ebonyi sannan ya mika wa wani kamfani.

Kazalika, kotun ta umarci Gwamnatin Ebonyi ta mayar wa kamfanonin Andrew Bishsopton da Partiner, Mauritz Walton da kudi miliyan 118 don cika sharuddan yarjejeniyar kwantaragi.

Har wa yau, kotun ta bukaci CBN ya zabtare Dala $29,854,856 da N100,000,000 daga asusun jihar kana ya mika wa kamfanin.

Bayanai sun nuna Gwamnatin Jihar Ebonyi ta bai wa kamfanin da lamarin ya shafa kwantaragi ne a 2016 kan kwato mata kudaden da aka cire daga asusunta ba bisa ka’ida ba.

Da yake yanke hukunci, Alkalin kotun Mai Shari’a Dalop Pam, ya ce Gwamnatin Ebonyi ba ta yi wa kamfanin na Andrew Bishsopton adalci ba, don haka dole a cire kudin daga lalitarta a biya su.