✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta ba DSS damar ci gaba da tsare Tukur Mamu

DSS ce ta bukacin hakan a gaban kotun

Wata Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta ba Hukumar Tsaro ta DSS damar ci gaba da tsare mai shiga tsakani da ’yan ta’addan da suka sace fasinjojin jirgin kasan Kaduna, Tukur Mamu, har nan da kwana 60 masu zuwa.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN), alkalin kotun, Mai Shari’a Nkeonye Maha, ce ta yanke hukuncin ranar Talata, bayan lauyan hukumar, Ahmed Magaji, ya roki kotun.

A cikin kunshin karar mai lamba FHC/ABJ/CS/1617/2022 mai dauke da kwanan watan 12 ga watan Satumban 2022, DSS ta bukaci kotun ta amince da bukatar tasu saboda su sami damar kammala bincikensu a kan dan jaridar.

Mamu, wanda hadimin fitaccen malamin addinin Musuluncin nan, Dokta Ahmed Gumi, ne ya kasance babban mai shiga tsakani da ’yan ta’addan da suka sace fasinjojin jirgin kasan Kaduna zuwa Abuja.

A karshen makon da ya gabata ne dai Kakakin hukumar ta DSS, Peter Afunanya ya ce hukumar ta gano abubuwa masu sosa rai a binciken da suka yi a gida da ofishin Tukur Mamun.

Afunanya ya kuma ce rahotannin da wasu mutane ke yadawa a kafafen yada labarai ba za su dauke hankalin hukumar daga binciken da hukumar ke yi a kansa ba.

An dai kama shi ne a makon da ya gabata a filin jirgin sama na Malam Aminu Kano da ke Kano, bayan an tiso keyar shi daga kasar Masar.

Ana dai zarginsa ne da hannu a wata badakalar kudaden kudin fansa da yawansu ya haura Naira biliyan biyu da ma wasu zarge-zargen.