✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta bayar da belin Bashir Dandago

Wakar cike take da cin zarafi da ashariya da tsinuwa ga dukkanin malaman Jihar Kano

Kotun Majistare da ke Kano ta bayar da belin fitaccen mawakin begen Manzon Allah (SAW), Bashir Dandago.

Kotun da ke zamanta a unguwar Nomansland, ta ba da belin mawakin ne bayan Gwamnatin Jihar Kano ta gurfanar da bisa zargin neman tayar da fitina da zagin malamai da kuma fitar da wata wakar da ke iya tayar da rikici kuma ba bisa ka’ida ba.

Da yake gabatar da kara, Lauyan Gwamnati, Barista Wada A. Wada ya shaida wa kotun cewa mawakin ya sakin wakar ba tare da tantancewa ba, wacce kuma ke cike da cin mutuncin mutane tare da tayar da fitina a cikin al’umma.

Sai dai mawaki Bashir Dandago ya musanta aikata laifin da ake tuhumar sa, wanda ya saba da sashe na 121 na ACJL.

Daga nan lauyansa, Barista Rabi’u Abdullahi ya nemi kotun da ta bayar da belin mawakin kuma alkalin Kotun, Mai shari’a Aminu Gabari ya amince.

Alkalin ya sanya sharadin sai mawakin ya gabatar da mutane biyu da za su tsaya masa, ciki har da Kwamandan Hisbah na Karamar Hukumar Gwale.

Har ila yau alkalin kotun ya dage sauraren shari’ar zuwa rabar 13 ga watan Afrilu, 2021.

Da yake yi wa Aminiya karin haske Shugaban Hukumar Isma’ila Tace Fina-finai da Dab’i ta Jihar Kano, Isma’ila Na’abba Afakallah ya bayyana cewa hukumar ta dauki matakin ne duba da yadda wakar ke cike da munanan kalamai da zagi wanda bai kamata ya fito daga mawaki kamarsa ba.

“Wakar cike take da kalamai munanan wanda mutum zai yi mamaki idan aka ce daga bakin mawaki mai hankali mai kuma shekaru irin nasa ta fito”

A cewar Afakallah, babu wani abu na fasaha a cikin wakar, sai zagin wasu bangarorin addini wanda hakan bai dace ba.

“Waqar cike take da zambo da cin zarafi da ashariya da tsinuwa ga dukkanin gamayyar malaman Jihar Kano da suka fito daga darikar Kadiriyya da Tijjaniyya da kuma Kungiyar Izala masu kalubalantar Abduljabbar a kan cin zarafin Ma’aiki (SAW).

Aminiya ta ruwaito cewa a baya ma Mawaki Bashir Dandago ya fuskanci hukuncin kotu saboda sakin wata waka ta zagi da cin zarafi ga tsohon Gwamnan Kano, Malam Ibrahim Shekarau.