✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta bayar da belin wadanda ake zargi da kisan Tolulope

Wanda ake zargi da kashe mace ta farko mai tuka jirgin saman soji a Najeriya ya samu beli

Wata Kotun Majistare da ke zamanta a Kaduna ta bayar da belin wasu ’yan uwa biyu da ake zargi da hatsarin motar da ya yi sanadiyyar mutuwar mace ta farko mai tuka jirgin sojin saman Najeriya, Tolulope Arotile.

A ranar 14 ga watan Yuli ne Rundunar Sojin Sama ta Najeriya ta mika wadanda ake zargin ga ’yan sanda domin fadada bincike da kuma gurfanar da su a gaban kuliya.

A ranar Laraba aka gurfanar da mutanen da suka hada da wanda ya tuka motar da ta take Tolulopen da dan uwansa, wanda shi ne mai motar a gaban Mai Shari’a  Benjamin Hassan.

Ana zargin wanda ya tuka motar da laifin tukin ganganci, tuki ba tare da lura ba, tuki ba tare da lasisi ba da kuma tuki ba amincewar mai mota ba.

Shi kuwa dan uwan nasa ana tuhumarsa da laifin da sakaci da haddasa hatsari ga mutane da kuma dukiya.

Dukkanninsu sun musanta zarge-zargen da ake musu.

Daga nan ne sai lauya mai shigar da kara Martins Danjuma Leo ya roki kotun da ta bayar da umarnin tsare wanda ya tuka motar a kurkuku kasancewar ’yan sanda na binciken zargi kisan kai a kansa.

Amma lauyan da ke kare shi, Aliyu Ibrahim Omachi ya kalubalanci hakan da cewa wannan ne karon farko da ya aikata laifi, kuma ya riga ya yi kusan makonni hudu a tsare

Mai shari’a Benjamin ya bayar da belin wanda ya tuka motar a kan Naira miliyan daya, sai kuma dan uwansa a kan Naira 500,000.

Kazalika, alkalin ya umarce su da su kawo mutane biyu da za su tsaya musu, wanda kowannensu yake zaune a yankin da kotun ke da hurumi kuma yake gudanar da halastaccen kasuwanci tare da gabatar da shaidar da za ta tabbatar da hakan ga kotun.

Alkalin ya kuma dage sauraron shari’ar zuwa 24 da kuma 26 ga watan Agusta.

Marigayiya Tolulope Arotile, wacce ita ce matukiyar jirgin sojin saman Najeriya mace ta farko ta rasu ne a 14 ga watan Yuli lokacin da motar wacce abokin karatunta ke tukawa ta take ta, yayin da suke tafiya da baya domin su gaisa da ita.

Dukkan mutane ukun da ake zargi tsofaffin abokan karatunta ne a makarantar sakandaren ‘ya’yan sojin sama da ke Kaduna.