✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Kotu ta bayar da sammacin damko Mahdi Shehu

Wata Babbar Kotun Shari’a da ke zamanta a kan titin Nagogo da ke Unguwar GRA a Jihar Katsina, ta bayar da umarnin aika wa Mahdi…

Wata Babbar Kotun Shari’a da ke zamanta a kan titin Nagogo da ke Unguwar GRA a Jihar Katsina, ta bayar da umarnin aika wa Mahdi Shehu sammacin tilasta shi ya bayyana a gabanta.

Umarnin da Kotun ta bayar ya biyo bayan kin bayyana a gabanta da Mahdi Shehu ya yi domin ci gaba da sauraron korafin da Dokta Mustapha Inuwa ya shigar a kansa kan zargin bata masa suna.

Dokta Inuwa wanda shi ne Sakataren Gwamnatin Jihar Katsina, ya na neman Kotun ta bi masa hakki kan zargin bata masa suna da Mahdi Shehu ya yi, bisa ga madogara ta sashe na 188 cikin dokokin Shari’a na Jihar Katsina.

A yayin sauraron karar, Mahdi ko Lauyansa ba su bayyana a gaban kotun ba, kuma ba su aiko wa da kotun wata sanarwa ko kuma wasika ta bayyana dalilin rashin halartar zaman kotun ba, wanda hakan ya nuna sun yi watsi da umarnin Kotun wadda ta gabatar musu tun a ranar 16 ga watan Dasimban 2020.

Da ya ke gabatar da jawabai, Lauyan wanda ya shigar da kara, Barrista A.S Ibrahim, ya roki kotun da ta ci gaba da sauraron karar ba tare da wanda ake kara ya gabatar da kansa ba duba da an riga da aika masa takardar gayyata.

Ya kuma roki Kotun da ta ba da umarnin cafke wanda ake kara saboda rashin bayyana a gaban kotu da kuma yin watsi da umarninta da ya yi.

A yayin da ya ke yanke hukunci, Alkalin da ke sauraron karar, Sagir Said Imam, ya amsa bukatar Barrista Ibrahim, inda ya ba da umarnin a cafke wanda ake tuhuma yayin da kuma ya dage sauraron karar zuwa ranar 13 ga watan Janairu.