✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Kotu ta daure Sufeton ‘Yan sanda a gidan yari

Kotun ta ce Sufeton 'yan sandan Najeriya ya ki martaba umarnin da ta ba shi.

Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, ta yanke wa Sufeto-Janar na ‘yan sanda, Usman Alkali Baba, hukuncin daurin wata uku a gidan gyaran hali saboda kin bin umarnin da kotun ta ba shi.

Mai shari’a Olajuwon, wanda ya yanke hukuncin, ya ce hakan ya biyo karar da wani tsohon jami’in dan sanda, Patrick Okoli ya shigar yana mai cewa an yi masa ritaya daga aiki ba bisa ka’ida ba.

Alkalin kotun ya ce a tsare Sufeton ‘yan sandan har na tsawon wata uku ko kuma ya bi umarnin da kotun ta yanke a ranar 21 ga watan Oktoba, 2011.

Kotun ta ce “Idan ya kammala wa’adin wata ukun ba tare da bin umarnin kotun ba za a sake tsare shi na tsawon wani lokacin.”

Mai shari’a Olajuwon ya bayyana cewa duk da cewa hukumar ‘yan sanda ta ba da shawarar a mayar da Okoli bakin aikinsa, amma Sufeton ‘yan sanda ya yi buris da umarnin kotun.

Wannan na zuwa ne mako uku bayan mai shari’a Chizoba Oji na wata babbar kotun Abuja, ta yanke wa Shugaban Hukumar Yaki da Yi Wa Tattalin Arziki Zagon Kasa (EFCC), Abdulrasheed Bawa hukuncin dauri a gidan yarin Kuje da ke Abuja.

Alkaliyar kotun ta bayyana cewa, Bawa ya raina umarnin kotun da ta bayar a ranar 21 ga watan Nuwamba, 2018, inda ta umarci hukumar da ta mayar wa wani mutum motarsa kirar Range Rover da kudi Naira miliyan 40.

Sai dai daga bisani Mai shari’a Oji ta yi watsi da hukuncin da aka yanke wa Bawa bayan sauraron hanzarin da shugaban EFCC ya gabatar.