✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta dage sauraron karar Sheikh Abduljabbar a Kano

An ba da umarnin ci gaba da tsare Malam Abduljabbar a gidan dan kande.

Wata Babbar Kotun Shari’a a Jihar Kano, ta dage sauraron karar Sheikh Abduljabbar Nasir Kabara zuwa 2 ga watan Satumban 2021.

A ranar Laraba ce Alkali Ibrahim Sarki Yola ya dage zaman sauraron karar bayan da aka yi zama na biyu tun fara shari’ar kan zargin malamin da kalaman batanci ga Annabi SAW.

Tun a ranar 16 ga watan Yuli aka yi zama na farko kan karar da Gwamnatn Jihar Kano ta shigar na zargin Malam Abduljabbar da kalamai na tunzura mabiya addinin Islama na hakika.

Kamfanin Dillancin Labarai NAN ya ruwaito cewa, Alkali Sarki Yola ya bayar da umarnin ci gaba da tsare Malam Abduljabbar a gidan dan kande.

A cewarsa, abubuwan da aka gabatar yayin zaman kotun na ranar Laraba ba su kai ga tsayar da hukunci a kan wanda ake tuhuma ba, lamarin da ya ce akwai bukatar ya yi nazari a kai.

Kazalika, lauyoyin gwamnati sun bukaci da a ba su dama su karanto sabbin tuhume-tuhume da suka je da su, lamarin da lauyoyin Malamin suka kalubalanta.

Barista Muhammad Saleh Bakaro wanda shi ne lauyan da yake jagorantar bangaren Abduljabbar, ya ce gaba daya lauyoyin SAN hudu da gwamnati ta dauko ba su da hurumi a tsarin dokar aikin lauya na tsaya wa a gaban karamar kotu.

“Daga Babbar Kotun Tarayya ne aka yarda manyan lauyoyi masu mukamin SAN su fara zuwa kotu.

“Sannan sabbin tuhume-tuhumen da suka bayar ya saba da tsarin dokar shariar Musulunci.

“Haka kuma, ba a yarda a sake shigar da tuhuma ko kara kan wata da ake saurara ba, bayan gabatar da shaidar farko a tsarin dokar Shari’ar Musulunci karkashin sashe na 2, 108 da na 126,” a cewar Bakaro.

Wasu bayanai sun ce lauyoyin gwamnati sun ce kamata ya yi lauyoyin Abduljabbar su dakata a gama karanto sabbin tuhume-tuhumen da ake yi wa wanda ake karar kafin su kawo wata suka kan lamarin.