✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Nnamdi Kanu zai yi bikin Kirsimeti da Sabuwar Shekara a hannun DSS

Lauyoyin Nnamdi Kanu sun yi barazanar sauya kotu saboda zargin rashin adalci.

Babbar Kotun Tarayya da ke sauraron shari’ar zargin shugaban haramtacciyar kungiyar ’yan a-waren Biyafra (IPOB) Nnamdi Kanu da ta’addanci zuwa ranar 19 da 20 ga watan Janairun 2022.

Nnamdi Kanu na fuskantar shari’a a gaban kotun da ke zamanta a Abuja ne bayan Gwamantin Tarayya ta gurfanar da shi bisa zargin ta’addanci, tayar da fitina da kuma yada karairayi kan Shugaba Muhammadu Buhari da sunan neman kafa kasar Biyafra.

Gabanin zaman kotun na ranar Laraba, an ga lauyoyin Kanu sun fice daga kotun a fusace tun kafin isowar alkalin da ke sauraron shari’ar, wato Mai Shari’a Binta Nyako.

Yayin zaman kotun, Nnamdi Kanu ya shaida wa Mai Shari’a Binta Nyako cewa jami’an tsaro na DSS sun hana lauyansa da ya zo daga Amurka shiga cikin kotun.

Daga baya Mai Shari’a Binta Nyanko ta sanar da dage ci gaba da sauraron shari’ar zuwa ranar 19 ga watan Janairun 2022.

A zantawarsa da manema labarai, lauyan Nnamdi Kanu mai suna Bruce Fein, ya yi zargin cewa shi kadai DSS ke neman hanawa shiga shari’ar kuma sau biyar ana hana shi ganin wanda yake karewa.

“Ni ne lauyansa na kasar waje, amma duk da tabbacin da aka bayar cewa wanda ake zargi zai iya ganin dukkan lauyoyinsa karo na biyar ke nan ana hana ni shiga wajensa,” inji shi.

Bayan dage zaman kotun, lauyoyin Kanu sun yi barazanar sauya kotu saboda zargin ba za a yi masa adalci ba.

“Da irin abin da muka gani a yau, ba ma zaton kotun nan za ta yi mana adalci,” a cewar wani daga cikinsu.