✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta dakatar da Ganduje daga sayar da wani asibiti a Kano

Mutanen unguwar ne suka maka gwamnati a gaban kotun

Babbar Kotun Jihar Kano da ke zamanta a titin Miller Road ta bayar da umarni ga Gwamnatin Jihar Kano da ta dakatar da yunkurin ta na sayar da wani asibiti da ke unguwar ’Yan Awaki da ke Kofar wambai a birnin Kano.

Tun da farko dai al’ummar unguwar ta ’Yan Awaki da adadinsu ya kai 113 ne suka mika kokensu ga kotun dauke da sa hannun jagoransu, Salisu Ibrahim Yan awaki, Kofar Wambai.

Mazauna unguwar sun nemi kotun ta hannun lauyansu mai suna Barista Badamasi Sulaiman Gandu, da ta hana Gwamnan Jihar, Abdullahii Umar Ganduje da Kwamishinan Shari’a na Jihar da Karamar Hukumar Birni da Kewaye daga daukar kowane mataki a kan filin.

Alkalin Kotun, Mai Shari’a Maryam Ahmad Sabo ta yi umarni da cewa Gwamnatin Jihar Kano ta dakatar da wannan kuduri har sai kotun ta kammala sauraron bangarorin biyu.

Har ila yau, kotun ta dage sauraren karar har zuwa ranar 23 ga watan Disamban 2022.

Rahotanni sun ce Gwamnatin na kokarin mallaka wa wasu mutane asibitin ne domin su mayar da shi shaguna lamarin da ya sa mazauna yankin suka dauki matakin shari’a. .