✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta dakatar da kamfanin jiragin sama na Najeriya daga fara aiki

Masu kamfanonin jiragen sama na Najeriya ne suka shigar da kara

A ranar Talata wata Babbar Kotun Tarayya mai zamanta a Legas, ta ba da umarnin dakatar da kamfanin jiragin sama na Najeriya (Nigeria Air) daga fara aiki.

Kotu ta ba da umarnin dakatawar ne biyo bayan karar da masu kamfanonin jiragen sama, karkashin kungiyarsu ta AON suka shigar a gabanta.

Wadanda lamarin ya shafa sun shigar da karar ce inda suke kalubalantar fifikon da Gwamnatin Tarayya ta bai wa kamfanin jirgin sama na kasar Habasha game da hannun jari na kashi 49 a sabon kamfanin nata.

Kamfanonin da suka shigar da karar sun hada da Azman Air da Air Peace da Max Air da United Nigeria da kuma kamfanin Top Brass.

Sannan wadanda aka shigar da su karar sun hada da kamfanin jiragin sama na Najeriya da na Habasha da Ministan Sufurin Jiragin Sama, Hadi Sirika da kuma Babban Lauyan Gwamnati.

Babbar Kotun, karkashin jagorancin Mai Shari’a A. Lewis-Allagoa ta ba da umarnin a gaggauta sauraron wannan kara.

Sai dai kuma, Ministan Sufurin Jiragen Sama, Hadi Sirika, ya ce Gwamnati za ta ci gaba da kokarin ganin jirgin na ta ya fara aiki duk da umarnin kotun.

Ya ce, “Na kamanta gaskiya wajen shirye-shiryen ganin jirgin ya fara aiki. Duk mai sha’awar zuba jari a kamfanin kofa a bude take.”