✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta hana Majalisa tsige Mataimakin Gwamnan Zamfara

Kotun ta kuma hana majalisar dakatar da mambobinta ’yan jam’iyyar PDP.

Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta dakatar da Majalisar Dokokin Zamfara daga yunkurinta na tsige Mataimakin Gwamnan Jihar, Mahdi Aliyu.

Alkalin kotun, Mai Shari’a Obiora Egwuatu ne ya ba da umarnin  a ranar Litinin lokacin da yake yanke hukunci a kan bukatar hakan da jam’iyyar PDP ta shigar, ta hannun lauyanta, Ogwu Onoja, mai mukamin SAN.

Alkalin, wanda kuma ya umarci wadanda ake karar da su guji duk wani yunkuri kan lamarin har zuwa lokacin da za ta yanke hukunci, ya kuma hana majalisar dakatar da mambobinta wadanda har yanzu suke jam’iyyar adawa ta PDP.

Kazalika, alkalin ya bukaci masu karar da su sanar da wadanda ake karar matsayin kotun kafin ranar Juma’a, sannan ya dage ci gaba da sauraron karar har zuwa ranar 23 ga watan Yulin 2021.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya rawaito cewa PDP na karar Hukumar Zabe ta INEC ne da jam’iyyar APC da Shugabannin Majalisar Dattijai Majalisar Wakilai da ta Jihar Zamfara da Gwamna Matawalle da kuma Babban Alkalin Jihar.

A kwanakin baya ne Gwamna Bello Matawalle ya sauya sheka daga jami’iyyar PDP zuwa APC mai mulki, amma Mataimakin nasa ya ki ya bi shi.

’Yan Majalisar Dokokin Jihar sun yi barazanar tsige Mataimakin saboda shirya wani gangamin siyasa da ya yi a Gusau, babban birnin Jihar a makon da ya gabata.