✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta dakatar da Yakubu Dogara saboda sauya sheka zuwa APC

PDP ce ta maka shi a gaban kotun tun da farko

Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Abuja ta dakatar da tsohon Kakakin Majalisar Wakilai, Yakubu Dogara, daga majalisar saboda sauya sheka zuwa jam’iyyar APC.

Yakubu Dogara, wanda ya taba shugabantar majalisar tsakanin shekarar 2015 zuwa 2019 yanzu haka dai shi ne yake wakiltar mazabar Tafawa Balewa/Bagoro a zauren majalisar.

A shekarar 2020 ce ya sauya shekar daga PDP inda ya yi hujja da tabarbarewar shugabanci da ya ce an samu a Jiharsa ta Bauchi, karkashin jagorancin Gwamnan Bala Mohammed.

An dai zabe shi shugabancin majalisar ce a 2015 karkashin APC, amma daga bisani ya sauya shekar zuwa PDP gabanin zaben 2019, bayan shugabancin Majalisar Dokoki ta Kasa ya samu rashin jituwa da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari.

Jam’iyyar PDP dai, wacce a karkashinta Yakubu Dokagan ya ci zabe a 2019, ce ta maka shi a gaban kotun tana neman a ayyana kujerarsa a matsayin haramtacciya kuma wacce babu kowa a kai saboda sauya shekar.

An dai shigar da karar ce bayan Babbar Kotun Tarayyar da ke Abuja da kori Gwamnan Jihar Ebonyi, David Umahi da Mataimakinsa, Kelechi Igwe, saboda komawa APC.

Da yake yanke hukuncin ranar Juma’a, alkalin kotun, Mai Shari’a Donatus Okorowo, ya ce tun bayan sauya shekar, Yakubu Dogara bai cancanci ci gaba da zama a kan kujerar ba, la’akari da sashe na 68(1)(g) na Kundin Tsarin Mulki.