✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta daure jami’in LASTMA na bogi

Dubuna ta cika bayan ya yi sojan gona a matsayin jami'in hukumar LASTMA ya karbar kudi a hannun masu ababen hawa a Legas

Kotu ta yanke wa wani matashi hukuncin daurin wata hudu a gidan yari kan laifin yin sojan gona a matsayin jami’in Hukumar Kula da Ababen Hawa ta Jihar Legas (LASTMA).

Kotun tafi-da-gindanka da ke zamanta a yankin Oshodi na jihar ta yanke wa matashin hukuncin ne ba tare da wani zabi ba, bayan kama shi da laifin tatsar kudi daga masu abubuwan hawa, musamman masu motocin haya.

Daraktan Hulda da Jama’a na LASTMA, Adebayo Taofiq, ya ce dubun matashin ta cika ne inda ya fada a hannun hukumar, a yayin da ya yi sojan-gona a matsayin jami’inta.

Ya bayyana cewa hukumar ta maka matashin a kotun ne kan zargin aikata laifuka biyu wadanda ka iya zama barazana ga zaman lafiyar jihar.

A yayin zaman kotun, mai gabatar da kara, Agbaje Oladotun, ya ce laifukan da matashin ya aikata sun saba wa Sashe na 168 (D) da na 78 na Dokokin Manyan Laifuka na Jihar Legas na 2015.