Daily Trust Aminiya - Kotu ta daure ma’aikacin banki shekaru 17
Subscribe

Kotu ta daure ma’aikacin banki shekaru 17

Wata Babbar Kotu a jihar Kano ta yanke wa wani ma’aikacin banki mai suna Rabi’u Hassan Dawaki, hukuncin daurin shekaru 17 a gidan kurkuku bisa aikata laifin zamba cikin aminci.

Mai shari’a Dije Abdu Aboki ce ta yanke hukunci a ranar Litinin bayan kotun ta samu Rabi’u da laifi kan tuhume-tuhume guda bakwai da aka yi masa da suke da alaka da zamba cikin aminci.

Haka kuma kotun ta yi watsi da tuhume-tuhume 21 da lauyan Hukumar Yaki da Rashawa ta EFCC ya yi masa sakamakon rashin baiwa kotun hujjojin da za ta gamsu da su.

Tun a ranar 26, ga watan Fabrairu na shekarar 2015 hukumar EFCC ta gurfanar da wasu mutun uku gaban Mai Shari’a Dije Abdu Aboki, wadanda aka gurfanar din sun hadar da Rabi’u Hassan Dawaki da Abdullahi Umar Rano da kuma Samuel Obende.

Hukumar ta EFCC ta gurfanar da su ne kan tuhume-tuhume guda 28 da suka hada da hada baki da cin amana da zamba cikin aminci da kuma karkatar da kudaden cikin asusun ajiya na jama’a da suka tasar ma naira miliyan 500.

Sai dai Aminiya ta samu cewa sauran mutum biyun da ake tuhuma; Abdullahi Umar Rano da Samuel Obende sun mutu kafin a kammala shari’ar.

More Stories