✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta daure magidancin da ya ‘zagi’ Ganduje a Facebook

Ana zargin mutumin ne da cin zarafin Gwamnan da ’ya’yansa a shafin Facebook.

Kotun Majistare da ke zamanta a unguwar Nomansland a Kano ta ba da umarnin sakaya wani magidanci a gidan gyaran hali bisa zargin bata sunan Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje.

Ana zargin mutumin, mai suna Mu’azu Magaji ne da cin zarafin Gwamnan da ’ya’yansa, Abdul’aziz da Balaraba, a shafinsa na Facebook.

An dai gurfanar da Mu’azu ne da wani Jamilu Shehu, wanda yanzu ya cika wandonsa da iska, a gaban kotun bisa zargin aikata laifuffuka da suka hada da hadin kai da zagi da tayar da hankalin al’umma da bata suna.

Laifukan dai a cewar takardar kunshin tuhumar ya saba da sassa na 97 da 114 da 391 da 399 na Kundin Manyan Laifuka.

Takardar karar ta ce a ranar 25 ga watan Oktoban 2021, Shugaban Karamar Hukumar Nassarawa, Auwal Shu’aibu ya kai kara sashen liken asiri na ’yan sanda (SIB) na Jihar inda ya yi korafi cewa wani mai suna Mu’azu Magaji Danbala da Jamilu Shehu, dukkaninsu mazauna Karamar Hukumar Kiru.

A ranar ne dai mutanen suka sanya hoton Gwamna Ganduje da ’ya’yansa Abdul’aziz da Balaraba, inda suka rubuta baro-baro cewa “Barayin Kano”.

Takardar karar ta ci gaba da cewa “Kun san cewa wanann abu da kuka yi zai iya haifar da tashin hankali a cikin Jihar.”

Sai dai wanda ake zargin ya musanta laifukan da ake zarginsa da shi inda kuma daga baya lauyansa ya roki kotun ta bayar da belinsa.

Sai dai kotun ta ki amincewa da bayar da belin wanda ake zargin saboda suka da bangaren lauyan masu kara ya yi, wato Barista Wada Ahmad.

Alkalin Kotun, Mai Shari’a Aminu Gabari, ya umarci Ofishin Binciken Manyan Laifuka na Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kano da ya bayar da kwafin karar kafin kotun ta san matsayar da za ta dauka akan ko za ta bayar da belin ko kuma akasin hakan.

Kotun ta kuma dage shari’ar zuwa ranar takwas ga watan Nuwamba, don ci gaba da shari’ar.