✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Kotu ta daure mahaifin da ya yi wa ’yar cikinsa fyade shekara 23

“Ya ba ta kudi ta zubar da cikin, amma ta ki”

Wata Kotun Majistare da ke Damaturu a Jihar Yobe ta yanke wa wani mahaifi hukuncin daurin shekara 25 a gidan gidan gyaran hali saboda samunsa da yi wa ’yar cikinsa fyade har ta sami juna-biyu.

Kotun dai ta yanke wa Umaru Alhaji Mustapha mai shekaru 43 hukuncin bayan ta same shi da aikata laifin a kan ’yar tasa mai suna Fatima mai shekara 18.

Alkalin kotun, Mai Shari’a Mohammed Bilyaminu, ne ya yanke hukuncin ranar Juma’a, bayan tabbatar da laifin da ake tuhumar mutumin da aikatawa.

Tun farko dan sanda mai shigar da kara ya shaida wa kotun cewa mahaifin yarinyar yana yawab saduwa da ’yar tashi ba tare da izininta ba, wanda ya haifar da ta sami ciki.

Sai dai ya ce jaririn ya mutu bayan haihuwa.

Dan sandan ya kuma ce wanda ake tuhumar bayan ya yi wa ’yar ciki, ya ba ta N25,000 domin ta zubar da shi, amma ta ki.

Haka kuma ita ma Fatima wadda aka yi wa tambayoyin ta ce mahaifinta ya fusata da ita matuka bayan ya fahimci cewa tana da ciki kuma ba ta bi umarninsa na zubar da shi ba, ya fara yi mata barazana.

Alkalin kotun, Mohammed Bilyaminu, ya ce abubuwan da ake zargin mutumin da su laifuka ne a karkashin sashe na 390 da na 283 na kundin penal code.

Don haka Ya yanke masa hukuncin daurin shekara biyar tare da biyan tarar dole ta N5,000 kan laifin lalata da kuma shekara 20 kan laifin fyade da tarar 10,000 bi-da-bi.

Kafin a yanke hukuncin, an baiwa wanda ake tuhuma damar neman a yi masa sassauci, inda ya bukaci kotun ta yi adalci da jinkai.

Ya ce yana da mahaifiyarsa tsohuwa da sauran masu dogaro da shi da ke karkashin kulawarsa.

Sai dai alkalin ya ce wanda aka yanke wa hukuncin na da kwana 30 don daukaka kara kan hukuncin.