✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta daure ‘Maman Boko Haram’ da wasu mutum 2 shekara 5

Kotun dai ta sake su da laifin damfarar sama da miliyan 71

Wata Babbar Kotun Jihar Borno da ke zamanta a Maiduguri ta daure Aisha Alkali Wakil, wacce aka fi sani da Maman Boko Haram da wasu mutum biyu shekara biyar, ba tare da zabin biyan tara ba.

Mai shari’a Aisha Kumaliya ce ta daure ta tare da Tahiru Saidu Daura da kuma Yarima Lawal Shoyode, bisa zambar Naira miliyan 71 da dubu 400.

Hakan ya biyo bayan tuhumar da Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Zagon Kasa ta EFCC shiyyar Maiduguri ta ke musu a gaban kotun.

Hukuncin dai shi ne kololuwar shari’ar da ta fara a ranar Litinin 14 ga watan Satumban 2020 inda aka sake gurfanar da wadanda ake kara a gaban kuliya bisa tuhume-tuhume biyu na hada baki da kuma karbar kudi ta hanyar karya.

Mama Boko Haram dai ita ce shugabar shirin, Tahiru Saidu Daura kuma Manaja, sai Prince Lawal Shoyode, Darakta na kasa.

An ce sun tuntubi Saleh Ahmed Sa’id na kamfanin Shuad General Enterprises Ltd domin ya kai musu buhunan wake 3,000 wanda kudinsu ya kai N71,400,000 bisa zargin aiwatar da kwangilar samar da kayayyaki.

Mai shari’a Kumaliya ta gano cewa sun aikata laifin da ya saba wa sashe na 1 (1) (b) da 1 (3) na dokar zamba da sauran laifuka masu alaka da zamba na shekarar 2006.

Sai dai mutanen sun ki amsa laifin da aka tuhume su da aikatawa.

A yayin shari’ar, lauyan mai shigar da kara, Mukhtar Ali Ahmed, ya gabatar da shaidu hudu tare da gabatar da takardu da dama wadanda aka shigar a matsayin bajekoli.

Da ta ke yanke hukuncin, Mai Shari’a Kumaliya ta ce, masu gabatar da kara sun tabbatar da tuhumar da ake yi wa wadanda ake kara kuma a sakamakon haka ta bayyana su da masu aikata laifin  da ake tuhumar su da aikatawa.

Don haka bisa ga dogara ga hukuncen da ke dauke da wannan kotun ta  yanke musu hukuncin daurin shekaru biyar a gidan yari ba tare da zabin biyan tara ba.

Alkalin ta kuma umarci wadanda aka yankewa hukuncin da su biya N30,500.000 a matsayin diyyar wadanda abin ya shafa.

A cewar ta, gaza yin hakan zai jawo musu karin shekara 10 a gidan yarin.