✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta daure Mataimakiyar Shugaban Kasar Argentina

Hukuncin kotun ya kuma haramta wa Fernández rike mukamin gwamnati har karewar rayuwarta.

Wata kotun kasar Argentina ta yanke wa Mataimakiyar Shugaban Kasar, Cristina Fernández, hukuncin daurin shekara shida a gidan yari.

Hukuncin kotun na ranar Talata ya kuma haramta wa Fernández rike mukamin gwamnati har ta bar duniya.

Kotu ta yanke mata wannan hukuncin ne bayan samun ta da lafin yin ruf da ciki kan Dala miliyan daya da aka ware don aiwatar da ayyukan gwamnati.

Duk da haka kotun ta wanke Fernández daga zargin mallakar haramtaccen kamfani, wanda da an same ta da laifi, hukuncinsa daurin shekara 12 ne a gidan yari.

Wannan shi ne karon farko da irin hakan ta faru a tarihin kasar ta Argentina.

Sai dai, wannan hukuncin ba zai tabbata ba har sai bayan Fernández’s ta daukaka kara, kuma ba ta yi nasara ba.

Haka nan, ba zai yiwu a kama ta ba saboda rigar kariyar da take sanye da ita albarkacin mulki.

Tuni dai magoya bayan Fernández suka sha alwashin haifar da cikas ga harkokin kasar ta hanyar zanga-zanga.