✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta daure matar da ta jagoranci yaki da hana mata tuki a Saudiyya

Shekara biyu ke nan da tsare Loujain al-Hathloul bayan zanga-zangar adawa da dokar

Kotun Manyan Laifuka ta kasar Saudiyya (SCC) ta yanke wa mai rajin kare hakkin mata Loujain al-Hathloul hukuncin daurin shekara biyar da wata takwas a kurkuku.

SCC ta yanke wa Loujain, wadda a baya ta jagoranci fafutikar soke dokar hana mata tuki a Saudiyya hukuncin ne saboda kama ta da aikata laifin ta’addanci.

“Ta aikata laifuka da damda da suka saba wa dokar hukunta laifukan ta’addanci”, inji hukuncin da kotun ta yanke a ranar Litinin.

Sai dai ta yi rangwamen wata biyu daga cikin watanni 10, “idan Loujain ba ta aikata laifi babban laifi ba a cikin shekara uku”.

Rahoton na kamfanin dillanci labarai na AFP bai bayyana ko wa’adin da aka yanke wa mata ya hada da lokacin da ta shafe a daure ba, ko kuma lokacin da za a sake ta.

Loujain na da damar daukaka kara cikin kwana 30 daga ranar da SCC ta yanke hukuncin.

A shekarar 2018 ne aka tsare ta tare da wasu mata masu fafutika, makonni kada kafin soke dokar da suka dade suna yak ana hana mata tuki a kasar.

Bayan an yi shari’ar farko ne aka tura shai’ar zuwa SCC wadda masu fafutika ke zargi da fakewa da yaki da ta’addanci tana yanke hukuncin daurin shekaru masu yawa domin muttsuke masu sukar gwamnati.

A baya Ministan Harkokin Wajen Saudiyya, Yarima Faisal bin Farhan ya shaida wa AFP cewa ana zargin ta da cin amanar kasar da ba wa kasashen abokan gaba sirrin kasar.

Iyalanta sun karyta zargin suka kara da cewa ce babu wata hujja da aka iya bayarwa da ke tabbatar da zargin.

Tuni dai aka saki wasu daga cikin matan da aka tsare tare da ita, bisa sharadi.

Ita da ragowar wasu kuma na tsare a kurkuku bisa zargin da kungiyoyin kare hakki ke cewa akwai kumbaya-kumbiya a ciki.