✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta daure matar da ta kashe 5 daga ’ya’yan cikinta 6 saboda kishi

Rahotanni sun nuna cewa babban dan matar ne kawai ya samu ya tsallake.

Wata kotu da ke zaune a birnin Wuppertal na kasar Jamus ranar Alhamis ta yanke wa wata mata da aka samu da laifin kashe ’ya’yan cikinta guda biyar hukuncin shekara 15 a gidan yari.

Matar, mai shekara 28 a duniya, wacce ke zaune a birnin Solingen na kasar Jamus, an sameta ne da laifin kashe ’ya’yan nata da ke tsakanin shekara daya zuwa takwas.

Rahotanni sun nuna cewa babban dan matar ne kawai ya samu ya tsallake.

Tun da farkon shari’ar dai, dan sanda mai shigar da kara ya ce matar ta daddanna ’ya’yan nata ne a cikin ruwa daya bayan daya, har suka mutu.

A cewarsa, matar ta fara fusata ne tun bayan da ta ga mijinta hoton mijinta da wata sabuwar budurwarsa.

Hakan ne ya sa ta tura masa rubutaccen sako cewa ba ta son ganin yaran a rayuwarta.

An dai gano gawarwakinsu ne a kan gado ranar 30 ga watan Satumban 2020.

Sai dai ta yi zargin cewa wani bako ne ya shigo gidan ya daddaureta sannan ya tilasta mata tura wa mijin nata sakon kafin ta kashe yaran.

A wani gwaji da likitocin kwakwalwa suka yi wa matar sun ce lafiyarta kalau, ba ta da matsalar tabin hankali.

Lauyan da yake kareta ya roki kotun da ta saketa saboda ya ce har yanzu babu wata cikakkiyar hujja da za ta nuna ita ta kashe su.

Kotun dai ta ce matar, wacce bayan aikata laifin ta tunkari jirgin kasa ta Dusseldorf amma ba ta mutu ba, ta kashe ’ya’yan nata; Melina da Leonie da Sophie da Timo da kuma Luca.

Daga nan kotun ta kuma damka babban dan matar, wanda shi kadai ya rayu, ga hannun kakarsa domin ta ci gaba da kula da shi. (NAN)