✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Kotu ta daure matashi shekara 2 saboda lalata allon kamfen din Atiku

Matashin ya ce N2,000 aka ba shi ya aikata laifin

Wata kotun yanki da ke garin Bukuru na Jihar Filato, ta yanke wa wani matashi hukuncin daurin shekara biyu a kurkuku, saboda samun shi da laifin lalata allon kamfe.

Alkalin kotun, Mai Shari’a Hycinth Dolnaan ne ya yanke hukuncin ranar Litinin kan matashin mai suna Gabriel Orupou, saboda lalata allon dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar a kan titin Zaramaganda da ke Karamar Hukumar Jos ta Kudu a Jihar.

A cewar takardar kunshin tuhumar da ake yi wa matashin, an gurfanar da shi ne kan zargin hada baki da kuma aikata ba daidai ba, laifukan da suka saba da sassa na 59 da na 313 na kundin Penal Code na Jihar.

An dai gurfanar da matashin ne tare da wasu mutum uku, wadanda har yanzu ba a gan su ba saboda sun cika wandonsu da iska.

Aikewa da matashin gidan kason dai ya biyo bayan hukuncin da aka yanke masa ranar Juma’a bayan ya amsa laifukan da ake zarginsa da aikatawa.

Sai dai lokacin da aka biya masa zarge-zargen ranar Litinin, matashin ya nemi afuwa, inda ya ce hayarsa aka dauka a kan N2,000 don ya lalata allon.

Ya ce wasu masu suna Musa da Baah da Danlami ne suka dauki hayar tashi, kuma yanzu haka dukkansu sun tsere.