✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta daure matashi shekara 3 kan satar abin wanke-wanke

Alkali ya bai wa matashi zabin biyan tarar N100,000.

Wata kotun Abuja mai zamanta a yankin Karu, ta daure matashi shekara uku a gidan yari kan laifin satar kayan kicin a Otel.

Sai dai Alkalin kotun, Umar Mayana, ya bai wa matashin zabin biyan tarar N100,000, kana ya gargade shi a kan ya guji aikta laifuka a nan gaba.

Mai laifin ya amsa tuhuma, ya kuma nemi kotun ta tausaya masa.

Tun da farko, lauya mai gabatar da kara, Mista Olarewaju Osho, ya fada wa kotun cewar an tsare tare da kai mai laifin ofishin ‘yan sandan Jikwoyi a ranar 28 Nuwamban 2022.

Ya ce yayin binciken ‘yan sanda, mai laifin ya amsa ya shiga “Bencalic Otel” inda ya sace wasu kayayyaki.

Laifin da lauyan ya ce hukuncinsa na karkashin sassa na 348 da 287 na ‘Penal Code’.

(NAN)