✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta daure tsohon jami’in MDD kan yi wa mata 20 fyade

Wani tsohon jami’in Majalisar Dinkin Duniya (MDD), Karim Elkorany, zai shafe shekara 15 a gidan yari bayan da kotu ta kama shi da laifin yi…

Wani tsohon jami’in Majalisar Dinkin Duniya (MDD), Karim Elkorany, zai shafe shekara 15 a gidan yari bayan da kotu ta kama shi da laifin yi wa mata sama da 20 fyade a yankin Gabas ta Tsakiya.

Bayanan da kotu ta samu sun ce, Elkorany ya shafe sama da shekara 20 yana yi wa mata fyade a yankin bayan da aka tura shi aikin jinkai a Iraki da Masar da sauransu.

An ce tsohon jami’in yakan bugar da matan da miyagun kwayoyi don kawar da hankalinsu kafin daga bisani ya yi musu fyade.

Akalla mata guda 20 aka ce Elkorany ya zakke wa ba da son ransu ba, galibinsu kuma kawayen juna ne.

Daga cikin matan da lamarin ya shafa kamar yadda bayanai suka tabbatar, har da ’yan jarida da ma’aikatan MDD.

A ranar Juma’a wata Babbar Kotun Manhattan a kasar Amurka ta yanke wa Elkorany hukuncin zaman kurkuku na shekara 15 bayan da ta kama shi da aikata laifin da aka tuhume shi.