✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta daure wani matashi shekara 1 kan satar waya a Kano

Matashin ya tsere da wayar bayan an ba shi aro da nufin zai kira wani.

Wata kotun Shari’ar Musulunci da ke zamanta a Jihar Kano ta yanke wa wani matashi dan shekara 27 hukuncin shekara daya a gidan gyaran hali bisa samun sa da laifin cin amana da kuma satar wayar da darajarta ta kai Naira 98,000.

Dan sanda mai shigar da kara, Isfekta Abdullahi Wada, ya shaida wa kotun cewa wani Isah Abdullahi daga unguwar Dorayi a Kano ne ya shigar da kara a ofishin ’yan sanda na Fagge a ranar 7 ga watan Yuli.

Ya ce, a wannan ranar ne mai karar ya bai wa wanda ake kara wayarsa kirar Samsung, wadda kudinta ya kai N98,000 domin ya yi waya, amma sai ya gudu da ita.

“Ana cikin haka sai mai karar ya gano cewa wanda ake kara ya lallaba ya gudu da wannan wayar.

“A yayin binciken ’yan sanda, wanda ake zargin ya amsa laifin sayar da wayar a kan kudi N70,000.”

Alkalin kotun, Ismail Muhammad Ahmed, ya yanke wa wanda ake kara hukuncin daurin shekara daya ko kuma zabin biyan tarar N17,000 tare da umartar sa da ya biya N98,000 ga wanda ya shigar da karar.