✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta daure ’yan sandan da aka kama tare da Abba Kyari shekara 6

Kotun dai ta ce za su shafe wa'adin ne a gidan gyaran hali na Suleja

Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta yanke wa biyu daga cikin ’yan sandan da ake zargi da laifin almundahanar kudade tare da korarren dan sanda, DCP Abba Kyari, hukuncin daurin shekara shida a kurkuku.

Da yake yanke hukuncin ranar Talata, alkalin kotun, Mai Shari’a Emeka Nwite, ya ce wadanda ake tuhumar, wato Chibunna Patrick Umeibe da Emeka Alphonsus Ezenwanne za su share hukuncin daurin ne a lokaci guda.

Wadanda ake zargi dai sun amsa laifunsu tun a ranar 22 ga watan Fabrairun 2022.

Sauran wadanda aka kamo tare da Abba Kyarin sun hada da ACP Sunday Ubua, da ASP Bawa James da Insfekta Simon Agirigba, da kuma John Nuhu, sai kuma John Umoru da ya cika wandonsa da iska.

Alkali Nwite ya ba da umarnin ci gaba da tsare ’yan sandan a babbar cibiyar gyaran hali ta Suleja da ke Jihar Neja.