✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta garkame wanda ake zargi da sace wa banki N11m a Legas

Wanda ake zargin da ke kare kansa a gaban kotu ya musanta aikata laifukan da ake tuhumarsa.

Wata Kotun musamman mai zamanta a garin Ikeja na Jihar Legas, ta bayar da umarnin tsare wani matashi a gidan gyaran hali kan zargin sace wa Bankin Fidelity kudi har Naira miliyan N11.27.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa, Hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa ta’annati ce ta gurfanar da matashin a gaban kotun.

Bayanai sun ce ana tuhumar matashin da laifuka guda biyu da suka hada da hadin baki da sata.

Tuni dai Alkalin kotun, Mai Shari’a Oluwatoyin Taiwo, ya ba da umarni a kai wanda ake zargin Gidan Gyaran Hali da ke Ikoyi a ajiye shi zuwa lokacin da za a bukaci a bayar da belinsa.

Kazalika, Mai shari’a Taiwo ya dage zaman sauraron karar zuwa ranar 8 ga Agusta mai zuwa.

Lauyan EFCC, Mista Nnemeka Omewa, ya ce wanda ake zargin ya saci kudi har Naira miliyan 11.27 mallakar Bankin Fidelity tare da hadin bakin wani abokinsa tun ranar 12 ga Yulin 2019.

Sai dai wanda ake zargin da ke kare kansa a gaban kotun, ya musanta aikata laifukan da ake tuhumarsa.