✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta hana Buhari da CBN kara wa’adin karbar tsoffin takardun kudi

Babbar Kotun ta hana Shugaba Buhari da Gwamnan CBN kara wa'adin amfani da tsoffin kudi

Babbar Kotun Birnin Tarayya ta hana Shugaba Buhari da Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele, kara wa’adin amfani da tsoffin takardun Naira da aka sauya fasalinsu.

Alkalin kotun, Mai Shari’a Eleoje Enenche ya kuma hana daukacin bankuna da ke Najeriya yin duk wata hulda da ta danganci tsoffin takardun kudin ko neman kara wa’adin amfani da su daga ranar 10 ga watan 10 ga watan Fabrairu da muke ciki.

Da yake sauraron ƙarar da wasu biyar daga cikin jam’iyyun siyasa 18 da ke Najeriya suka shigar, alkalin ya bukaci shugabannin bankuna da jami’ansu su kawo dalilan da za su hana a kama su da kuma gurfanar da su a gaban kotu kan zargin su da yin zagon kasa ga tattalin arziki, bisa yadda suke boye sabbin takardun Naira 1,000 da N500 da kuma N200 da CBN ya sauya wa fasali ya kuma ba su, amma suke kin ba wa mutane.