✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta janye umarnin hana Ganduje karbo bashin N10bn

Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Kano ta umarninta na hana Gwamnatin Jihar Kano ciyo bashin Naira biliyan 10 domin sanya kyamarorin tsaro na…

Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Kano ta umarninta na hana Gwamnatin Jihar Kano ciyo bashin Naira biliyan 10 domin sanya kyamarorin tsaro na CCTV a jihar.

Da farko kotun ta hana gwamnatin ciyo bashin, bayan karar da Kungiyar Kano First Forum (KFF) ta shigar tana kalubalantar gwamnatin jihar, saboda rashin bin wasu ka’idoji na karbar bashi.

KFF ta hannun lauyanta, Barista Badamasi Sulaiman, ta bayyana shirin gwamnan jihar na ciyo bashin a matsayin haramtacce saboda ya saba da Dokar Karbar Bashi ta Ofishin Kula da Basussuka ta Shekarar 2003 da dokar Ma’aikatar Kasafin Kudi ta 2007 da kuma Dokar Karbar Bashi ta Jihar Kano ta 1968.

Amma lauyoyin Gwamnatin Jihar Kano karkashin jagorancin Barista Muhammad Dahuru suka nemi kotun ta jingine wancan umarni na dakatarwar da ta yi tunda farko.

Alkallin kotun, Mai Shari’a Abdullahi Muhammad Liman, ya bayyana cewa kotu tana da damar ta jingine umarnin da ta bayar bayan tsawon kwana 14.

Ya kuma umarci masu kara da su ci gaba da kes dinsu a gaban kotun Abuja saboda kotunsa za ta tafi hutu.

A nasa bangaren, lauyan KFF, Barista Badamasi Sulaiman, ya bayyana cewa duk da cewa kotun ta jingine umarninta na baya, hakan ba ya nufin gwamnati za ta ci gaba da neman bashin har sai an kammala shari’ar.

A kwanakin baya ne Majalisar Dokokin Jihar Kano ta sahalewa gwamnatin jihar ta karbo bashin Naira biliyan 10 daga Bankin Access don sayen na’urar tsaro ta CCTV da gwamnatin ta ce za ta sanya a titunan da ke kwaryar birnin Kano.