✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta kori da karar neman sallamar shugaban ’yan sanda

Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ya kori karar ce bisa hujjar cewa wanda ya shigar da karar, Michael Sam Idoko, ba shi da hurumin…

Kotu ta kori karar da aka shigar gabanta na neman ta tilasta wa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya sallami Sufeto-Janar na ’Yan Sandan Najeriya, Usman Alkali Baba, bayan ya cika shekarun yin ritaya daga aiki.

Mai Shari’a J.K. Omotosho na Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ya kori karar ce bisa hujjar cewa wanda ya shigar da karar, Michael Sam Idoko, ba shi da hurumin yin hakan.

Alkalin ya ce cikar shugaban ’yan sandan shekarun yin ritaya daga aiki bai hana shi cin gajiyar wa’adinsa na shekara hudu da Dokar Aikin Dan Sanda ta 2020 ta tanadar ba.

Idoko ya shigar da kara ne yana mai dogaro da cewa dole ne Usman Alkali Baba ya yi ritaya daga aiki idan ya cika shekara 60 da haihuwa ko kuma shekara 35 a bakin aiki.

Ya yi karar Alkali; Majalisar Aikin Dan Sanda, Shugaba Buhari da Antoni-Janar na Kasa ne da cewa ci gaba da zaman Baba a matsayin shugaban ’yan sandan bayan ya kai shekarun yin rita ya ci karo da sashe na 215(a) na kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999.