✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta kori karar da EFCC ta kai tsohon kakakin PDP

Alkalin ya ce tuhumar da ake yi wa Metuh a cikin karar da aka shigar tozarta shari’a ne.

Wata Babbar Kotun Tarayya ta kori karar da Hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa ta’annati ta kai Oliseh Metuh, tsohon kakakin jam’iyyar PDP.

Babbar Kotun da ke zamanta a Abuja ta kori karar da EFCC ta shigar a gabanta ne ranar Litinin, wadda ta nemi kotun ta sake sauraron shari’ar.

A jawabinsa a lokacin da ya ke yanke hukunci, Mai shari’a Emeka Nwite ya ce, ya kori karar ce saboda tuhumar da ake yi wa Metuh a cikin karar da aka shigar gabansa tozarta shari’a ne.

Alkalin ya bayyana cewa, tun da batun shari’ar na kotun koli, sake kawo batun gabansa domin sake wata shari’ar, tozarta tsarin shari’a ne.

Hukumar EFCC ta kai karar Oliseh Metuh ne a gaban Kotun tana bukatar kotun ta sake yi wa Metuh shari’a shi da kamfanins Destra Investmet Ltd.

A ranar 16 ga watan Disamba na shekarar 2020, Kotun Daukaka Kara ta Abuja ta soke wani hukuncin Babbar Kotun da ta daure Metuh shekara bakwai a bisa laifin halasta kudin haram.

Tun da farko dai Babbar Kotun ta daure Metuh bisa zargin cewa ya karbi Miliyan 400 daga tsohon Mai ba Shugban Kasa Shawara Kan Sha’anin Tsaro, Kanar Sambo Dasuki mai ritaya, a gabannin zaben Shugaban Kasa na shekarar 2015.

Ana zargin Dasukin ya ba shi kudin ne ba tare da bin ka’idojin bayar da kwangila ba ko kuma tsarin aiwatar da aiki.