✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta mayar da Sagagi a matsayin shugaban PDP na Kano

Ta dage zaman kotun zuwa ranar Juma’a, 13 ga watan Mayu domin ci gaba da sauraron karar.

Wata Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Abuja ta mayar da Shehu Sagagi a matsayin shugaban jami’yyar PDP na Jihar Kano.

Haka kuma kotun ta mayarwa da shugabannin jam’iyyar PDP na Kananan Hukumomi 44 mukamansu har zuwa lokacin da za a yanke hukunci matabbaci a gabanta.

Da yake yanke hukunci kan lamarin a ranar Alhamis, Mai shari’a Taiwo O. Taiwo, ya amince da dukkan bukatun shugabannin da Sagagi ke jagoranta tare da gargadin shugabancin jam’iyyar PDP na kasa kan daukar duk wani mataki da zai kawo musu cikas.

Ana inya tuna cewa a ranar 29 ga watan Maris ne mai shari’a Taiwo ya bayar da umarnin hana jam’iyyar rusa kwamitin rikonta har sai an yanke hukunci.

Sai dai a wannan rana, Kwamitin Gudanarwa na Kasa na jam’iyyar PDP, ya yi zargin cewa, sun kauce wa bin umarnin kotu, inda suka yi gaba da rusa kwamitocin zartarwa na jihohi da kananan hukumomi da na gundumomi tare da kafa kwamitin riko na mutum 7 a jihar.

Sai dai Hukumar Zabe ta Kasa INEC, ta yi watsi da kwamitin riko da jam’iyyar ta tura, bisa bin umarnin mai shari’a Taiwo, wanda ya hana jam’iyyar yin katsalandan ga shugabannin zartarwa a matakin jihar da kananan hukumomi.

Yayin da aka fara sauraron karar ce a ranar 7 ga Afrilu, lauyan PDP, Adedamola Fanokun ya musanta cewa jam’iyyar ta kafa wani kwamitin riko a Kano.

Kazalika, da alkalin ya tambaye shi game da rantsar da sabon kwamitin riko, lauyan ya ce babu abin da ya faru.

Sai dai ta sake sauya matsaya a ranar Alhamis, inda wani sabon lauya na jam’iyyar PDP, AO Dada, ya bayyana cewa jam’iyyar ta kafa kwamitin rikon kwarya kuma tana rokon kotu da ta tabbatar da hukuncin da jam’iyyar ta yanke.

Lauyan ya bayar da misali da hukuncin da aka yanke wa alkali daya a kan wani shari’a makamancin haka, amma alkalin ya musanta cewa shari’o’in sun bambanta.

A kan haka ne mai shari’a Taiwo ya dage zaman kotun zuwa ranar Juma’a, 13 ga watan Mayu domin ci gaba da sauraron karar.