✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Kotu ta raba auren shekara 1 saboda rashin soyayya

Wata Kotun Shari’ar Musulinci da ke Ilorin, Jihar Kwara ta raba wasu ma'aurata da aka daura aurensu watanni 12 da suka gabata.

Wata Kotun Shari’ar Musulinci da ke Ilorin, Jihar Kwara ta raba wasu ma’aurata da aka daura aurensu watanni 12 da suka gabata.

Alkalin kotun, AbdulQodir Umar, ya ce matar mai suna Roimat Qodir ta roki kotun ta kashe aurenta da mijinta Qodir AbdulRazak, saboda ba ta son sa.

Bayan alkalin ya tambaye ta ko tana da juna biyu, ta musanta hakan.

Shi ma dai mijin ya bayyana wa alkalin cewa ya amince da bukatar matar, kuma ko a lokacin ta so za ta iya tafiya.

A karshe dai kotun ta raba auren, tare da bai wa matar umarnin yin iddar watanni uku kamar yadda addinin Musulinci ya tanada.