✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta rushe tsagin Ganduje na shugabancin APC a Kano

Kotun ta rushe jagorancin Abdullahi Abbas, ta tabbatar da na Ahmadu Zago.

Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja a ranar Talata ta soke zaben da tsagin Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya shirya na zaben shugabannin jam’iyyar APC.

Alkalin kotun, Mai Shari’a Hamza Mu’azu ya kuma ce zaben da tsagin Sanata Ibrahim Shekarau ya gudanar shi ne halastacce a Jihar.

Hakan dai na nufin kotun ta rushe jagorancin jam’iyyar karkashin Abdullahi Abbas, tare da tabbatar da na Ahmadu Haruna Zago.

A cewar kotun, tsagin Sanatan da ke da mutum bakwai, wanda ake wa lakabi da “G-7”, shi ne ya gudanar da zaben da wakilan jam’iyyar APC su bakwai suka sanya wa hannu.

Rahotanni sun ce wanda ke karar shi ne Muntaka Bala Sulayman, tare da wasu ’ya’yan jam’iyyar su kimanin 17,980.

Wadanda ake karar kuma sun hada da jam’iyyar APC da Shugabanta na riko, Mai Mala Buni da Sakatarenta, Sanata John Akpanudoedehe da kuma Hukumar Zabe ta Kasa Mai Zaman Kanta (INEC).

Kotun dai ta ce zabukan da tsagin Sanata Shekarau ya shirya shi ne halastacce.

Lauyan da ya wakilci masu karar shi ne Barista Nuraini Jimoh, SAN yayin da su kuma wadanda ake karar sune Barista Sule Usman, SAN da M.N. Duru da kuma Mashood Alabelewe.