✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta sa a tsare Bakanuwar da ake zargi da kisan jikanta

Ana zarginta da ba jikan nata gishirin kunshi a baki

Wata kotun majistare a jihar Kano ta aike da wata mata mai suna Hauwa Ibrahim gidan gyaran hali saboda zargin da ake yi mata na hallaka jaririn jikanta.

Kotun, mai lamba 45 da ke zamanta a unguwar Nomansland a Kano da ke karkashin jagorancin Mai Shari’a Haulatu Magaji Kankarofi, ce ta yanke hukuncin ranar Litinin.

Lamarin ya faru ne a Garin Tungar Bala da ke yankin Karamar Hukumar Bagwai ta Jihar Kano.

Tun da farko, an gurfanar da kakar ne a gaban kotun bisa tuhumarta da hallaka yaron amaryar danta, wai don tana zuwa ta fara da haifar namiji, sabanin uwargidan da take haihuwar ’ya’ya mata, ba ta taba haihuwar da namiji ba.

Bayan an haifi jaririn ne sai ita Hauwa wacce uwar miji ce ga amaryar, ta dauko gishirin kunshi ta sanya wa jikan nata a cikin bakinsa a daidai lokacin da mahaifiyar yaron ta shiga wanka.

Lamarin dai ya janyo jaririn ya shiga wani hali, inda aka garzaya da shi asibiti domin ceto rayuwarsa, amma ya ce ga garinku nan.

Bayan da mai gabatar da kara, Barista Ahmed ya tambaye ta ko ta aikata laifin, inda nan take babu bata lokaci ta amsa aikatawa.

Kotun dai ta sanya ranar hudu ga watan Oktoban 2022 domin ci gaba da sauraran karar, sannan ta aike da ita zuwa gidan gyaran hali.