✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta sa EFCC ta kawo mata AA Zaura

EFCC ta yi karar dan takarar ne bisa zargin sa da damfarar wani dan kasar Kuwait Dala miliyan 1.3.

Kotu ta umarci Hukumar Yaki da Masu Karya Tattalin Arziki (EFCC) ta kawo mata dan takarar Sanatan Kano ta Tsakiya, Abdulkareem Abdussalam Zaura (wanda aka fi sani da AA Zaura) kan zargin almundahana.

Mai Shari’a Mohammad Nasiru Yinusa, ya bayar da umarnin ne a ranar Alhamis bayan EFCC ta bayyana cewa wanda ake zargin bai halarci zaman kotun ba, kamar yadda bai halarci wasu zama biyu da ta yi kan batun a baya ba.

EFCC ta yi karar dan takarar ne bisa zargin sa da damfarar wani dan kasar Kuwait Dala miliyan 1.3.

A ranar Alhamis aka shirya gurfanar da shi a gaban kotu, bayan ta soke hukuncin baya da ya wanke shi daga zargin, ta sa a sake gurfanar shi.

A zaman kotun na ranar Alhamis, lauyan wanda ake zargin, Ibrahim Waru, ya shaida mata cewa an dage zama ne domin kabar bayanan bangarorin kan matsayin wajibcin zuwan wanda ake zargi kotu kafin ta saurari karar da ke kalubalantar huruminta na sauraron karar.

Sai dai lauyan EFCC, Abdulkareem Arogha ya shaida wa kotun cewa bai kamata ta saurari bukatar AA Zaura ba tunda bai halarci zaman ba.

Ya ce, “Muna kokarin ganin mun kawo shi kotu,” kamar yadda ya fada a lokacin da yake kalubalantar bukatar bangaren da ake kara.

Da yake yanke hukunci, Alkali Yinusa ya ba da umarnin a kawo wanda ake zargin, idan kuma ba a yi hakan ba, kotun za ta tabbatar an bi matakan da suka dace.

Ya ce wajibi ne halartar zaman kotu ga duk wanda ake zargi da aikata babban laifi kuma wajibi ne a karanta tuhumar da ake masa a gabansa kafin a fara shari’ar.

“Babu wani umarni na Kotun Daukaka Kara ko Kotun Koli da ya hana kotu yin aikinta a kan wannan batu,” in ji alkalin.

Daga nan ya dage zaman zuwa ranar 5 ga watan Disamba, tare da umarntar masu kara su kawo wanda ake karar a ranar zaman na gaba.

Idan ba a manta ba a zaman kotun na bayan EFCC ta bayyana wa alkali cewa ta kasa gano inda wanda ake zargin yake.

Bayan zaman kotun, lauyan AA Zaura, Ibrahim Waru, ya ce za su yi nazarin hukuncin kotun, su yanke shawara kan daukaka kara.

Lauyan EFCC ya ki yi magana, amma wanna wani daga cikin jami’ansa ya shaida wa wakilinmu a sirrance cewa nan da kwanaki hukumar na iya tsare AA Zaura, saboda ba ta da tabbacin zuwansa zama mai zuwa ba.