✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta sa ranar yanke hukunci kan ko Atiku ya cancanci tsayawa takara

Kotun dai za ta yanke hukunci a kan cancantar takarar tasa.

Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, a ranar Litinin, ta sanya ranar 21 ga watan Fabrairun 2022 domin yanke hukunci kan ko tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar ya cancanci tsayawa takarar Shugaban Kasa ko a’a.

Alkalin kotun, Mai Shari’a Inyang Ekwo ne ya sanya ranar, bayan kammala sauraron muhawara tsakanin lauyoyin bangarorin biyu.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya rawaito cewa wani kamfani mai zaman kansa mai suna EMA ne ya maka Atikun da jam’iyyar PDP da hukumar zabe (INEC) da kuma Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya a gaban kotun.

Kamfanin dai na kalubalantar cancantar Atikun ta tsayawa takarar Shugaban Kasa, bisa hujjar cewa ba asalin dan Najeriya ba ne ta nasabar haihuwa.

Ya roki kotun da ta yi la’akari da tande-tanaden sassa na 25(1) da (2) da kuma 131(a)na Kundin Tsarin Mulki wajen hana shi takarar.

A baya dai Gwamnatin Jihar Adamawa ta roki kotun da ta saka ta cikin wadanda ake tafka shari’ar da su, inda a ranar 27 ga watan Yulin 2021 kotun ta maince da hakan.

Jihar dai ta shaida wa kotun cewa Atikun ya cancanci tsayawa takara, kuma har ya taba jagorantar Jihar da kuma zama Mataimakin Shugaban Kasa na tsawon shekara takwas.

To sai dai lauyan masu kara, Oladimeji ya ce ko da yake a Najeriya aka haifi Atiku, hakan ba yana nufin shi dan Najeriya ba ne.

A cewarsa, kasancewar an yi kuskure a baya, ba ya nufin a sake maimaita hakan a yanzu.

Daga nan ne Mai Shari’a Ekwo ya dage ci gaba da sauraron karar zuwa ranar 21 ga watan Fabrarirun 2022 don yanke hukunci. (NAN)