✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu Ta Sake Ba Da Belin Wanda Ya yi Garkuwa Da Yayarsa A Zariya

Kotu ta shardanta masa kawo wanda zai tsaya masa wanda ke da N10m a banki da kuma gida mai wannan kimar

Kotu ta ba da belin wani matashi da ke ake zargi da yin garkuwa da yayarsa domin karbar kudin fansa a yankin Zariya a Jihar Kaduna.

Babbanr Kotun Jihar Kaduna mai zama a Dogarawa ta bayar da belin matashin ne a bisa dalilin rashin lafiya.

Alkalin kotun, Mai Shari’a Kabir Dabo ya ce wanda ake zargin na fama da matsanancin tari wanda kotu ke ganin mahalarta shari’ar na iya kamuwa da ita.

Ya ci gaba da cewa a duk lokacin da za a gabatar da shi, sai ya yi amfani da abin kariya don saboda tarin da yake yawan yi babu kakkautawa.

Belin da kotu ta bayar ya shardanta wa matashin kowa wanda zai tsaya masa, wanda kuma dole sai yana da gida da kudinsa ya kai Naira miliyan 10 kuma zai ajiye takardun mallakar gidan.

Ka’ida ta biyu ita ce dole sai wanda zai tsaya wa wanda ake zargin yana da akalla Naira miliyan 10 a asusun ajiyarsa na banki.

Alkalin kotun ya ce belin da ya bayar zai ba shi damar neman maganin ciwon da ke damun sa kafin ranar da za a ci gaba da sauraron shaida na karshe daga bangaren masu gabatar da kara.

Kotun ta bayar da belin a karkashin sashi na 36(5) na dokar shekarar 1999 da sashi na 174(1) da (2) da (c) na sashin dokar manyan laifuka ta Jihar Kaduna.

A halin da ake ciki kotu ta tafi hutu sai ranar 19 ga watan Satumba 2022 kuma shari’ar za ta ci gaba da gudana a ranar 18 ga watan Oktoba, 2022.