✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta saki dukkan wadanda suka kashe tsohon Fira Ministan Indiya

An sake su ne bayan sun shafe sama da shekara 30 a tsare

Wadanda ake zargi da kisan tsohon Fira Ministan Indiya, Rajiv Gandhi, a shekarar 1991 sun shaki iskar ’yanci bayan Kotun Kolin Kasar ta ba da umarnin sakin su gaba daya.

Mai shekara 46 a wancan lokacin, Gandhi, wata ’yar kuna bakin wake ce ta kashe shi yayin wani gangamin siyasa a jihar Tamil Nadu ta kasar.

An zargi ’yan kungiyar aware ta LTTE masu dauke da makamai na kasar Sri Lanka a lokacin da kisan tsohon Fira Ministan.

Kotun Kolin dai ta saki mutum shida na karshen da aka samu da laifin kisan bayan da ta ce ta gamsu kunnuwansu sun yi laushi bayan sun shafe sama da shekara 30 a gidan kaso.

Uku daga cikin wadanda aka kashe din, Nalini Sriharan da mijinta Murugan da kuma Santhan, sun fita daga gidan kason da ke garin Vellore ranar Asabar, wanda ke da nisan kilomita 140 daga babban birnin lardin na Chennai, kamar yadda wakilin Kamfanin dillancin Labaran Faransa (AFP) ya rawaito.

Kafafen yada labaran yankin sun rawaito cewa ragowar mutum ukun, Robert Pais da Jaikumar da kuma Ravichandran, sun fita daga gidan yarin ne a gidajen kason da ke biranen Chennai da Madurai na jihar.

Uku daga cikin mutum shidan dai an yanke musu hukuncin kisa kafin daga bisani a sassauta musu hukuncin.

Rajiv Gandhi, wanda shi ne Fira Ministan Indiya mafi karancin shekaru da ya gaji mahaifiyarsa, Indira Gandhi ne, inda ya dare karagar mulkin kasar a shekarar 1984.