✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta saki yarinyar da ta kashe wanda zai yi mata fyade

Kotun Majestari da ke zama a Yaba a jihar Legas ta sallami wata yarinya mai shekaru 15 da aka tuhuma da kashe abokin mahaifinta mai…

Kotun Majestari da ke zama a Yaba a jihar Legas ta sallami wata yarinya mai shekaru 15 da aka tuhuma da kashe abokin mahaifinta mai shekaru 51 da ya yi yunkurin yi mata fyade.

Alkalin kotun, Philip adebowale Ojo ya kori karar kisan kan da ‘yan sandan suka shigar a kan yarinyar ‘yar aji uku na Babbar Makarantar Sakandare (SSS3) biyo bayan shawarar da Sashen Gurfanar da Masu Laifi na Antoni janar (DPP) ya bayar.

A ranar 24 ga watan Maris, 2020 Sashen Binciken Manyan Laifuka na ‘yan sandan (SCIID) ya shigar da karar zargin yarinyar da kashe mutumin mai suna Babatunde Ishola a ranar 7 ga watan na Maris.

Lamarin dai ya faru ne a gidan mamacin a yankin Aboru, inda yake aikin gadi a wata makaranta.

A wancan lokacin rundunar ‘yan sandan ta sami umarnin tsare yarinyar a gidan gyara halinka na mata da ke Idi-Araba a bayan kotu ta dage sauraron karar.

Alkalin kotun ya wanke wadda ake zargin tare da sallamar ta. Ya kuma ce duk mai ganin an tauye hakkin wani a shari’ar sai ya tuntubi Daraktan Dukumar DPP, Mahmud Hassan.

A tsokacin da iyayen yarinyar suka yi bayan kammala shari’ar, sun bayyana godiyarsu ga gwamnatin jihar Legas da hukumomin da suka yi tsayin daka har ‘yar tasu ta sami kubuta.