✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta soke dakatar da ‘yan majalisar da ke adawa da tube Sarki Sanusi

Babbar Kotun Tarayya da ke zama a Kano ta soke dakatarwar da aka yi wa ‘yan majalisar dokokin jihar biyar wadanda suka ki goyon bayan…

Babbar Kotun Tarayya da ke zama a Kano ta soke dakatarwar da aka yi wa ‘yan majalisar dokokin jihar biyar wadanda suka ki goyon bayan tube tsohon Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II.

A ranar 15 ga watan Maris ne Majalisar Dokokin Jihar Kano ta dakatar da ‘yan majalisar bisa zarginsu da dauke sandar majalisar a lokacin zaman sauraron bincike da kuma sauke  tsohon Sarkin.

Alkalin kotun Mai Shari’a Alagoa ya ce  dakatarwar ba ta bisa ka’ida  kuma ta saba wa kundin mulkin kasa.

Don haka ya bada umarnin a biya ‘yan majalisun hakkokinsu da suka hadar da albashinsu da kudin alawus-alwaus nasu na tsawon lokacin da aka dakatar da su.

‘Yan majalisu biyar da lamarin ya shafa su ne wadanda suka ki goyon bayan cire tsohon sarkin Kano Muhammadu Sanusi II a ranar 16 ga watan Maris, lamarin da ya janyo hayaniya a zauren majalisar.

‘Yan majalisar da lamarin ya shafa sun hadar da  Garba Yau Gwarmai mai wakilta mazabar  Kunchi/Tsanyawa, da  Labaran Abdul Madari  da ke wakiltar mazabar Warawa, sai Isyaku Ali Danja mai wakiltar mazabar  Gezawa, da Mohammed Bello da ke wakiltar mazabun Rimingado da Tofa, sai Salisu Ahmed Gwangwazo mai wakiltar mazabar Kano Municipal.